IQNA

22:51 - November 19, 2020
Lambar Labari: 3485382
Tehran (IQNA) sakataren harkokin wajen Amurka ya kutsa kai a cikin yankin tuddan Golan na kasar da Isra’ila ta mamaye.

Jaridar Aldiyar ta bayar da rahoton cewa, a wani mataki na tsokana a karshen mulkin Donald Trump, a yau sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kutsa kai a cikin yankin tuddan Golan na kasar da Isra’ila ta mamaye.

Wannan na zuwa ne a  daidai lokacin da ya rage wata daya da ‘yan makonni Trump ya fice daga fadar white house bayan kayin da ya sha a zaben shugaban kasa, da nufin tabbatar wa duniya cewa gwamnatinsa gwamnati ce ta hidima ga yahudawan Isra’ila.

A nata bangaren gwamnatin kasar Syria ta bayyana cewa, wannan mataki bai zo mata da mamaki ba, domin kuwa babban abin da gwamnatin Trump ta aiwatar baki daya  a cikin shekaru hudu, shi ne mara baya ga ayyukan ta’addancin Isra’ila a kan al’ummomin yankin.

Shi ma a nasa bangaren babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Ahamd Abul Ghiaz ya bayyana cewa, wannan ziyara da Pompeo a cikin yankin Golan na Syria da yahudawan Isra’ila suka mamaye abin Allawadai ne, kuma hakan ba zai taba halasta wa Isra’ila mallakar tuddan Golan na kasar Syria ba.

 

3936217

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: