IQNA

23:47 - November 21, 2020
Lambar Labari: 3485386
Tehran (IQNA) iyalan marigayi Abdulbasit Abdulsamad sun bayar da kyautar kusuwansa na karatun kur’ani ga gidan rediyon kur’ani na Masar.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, an mika wadannan kasusuwa ne tare da halartar wasu daga cikin jami’ai na gidan rediyon kur’an, a daidai lokacin da ake shirin cikar shekaru 32 da rasuwarsa a ranar 30 ga watan Nuwamban 2020 da muke ciki.

Shugaban bangaren kula da tsoffin kayan tarihi da adana sun a cibiyar Azhar Abdulkarim Saleh, tare da Tarik Abdulbasit dan marigayi Abdulbasit, gami da wasu jami’ai na gidan rediyon kur’an da kuma ma’aikatar kula da harkokin addini ta Masar sun halarci wurin.

An harhada wadanan kasasuwa ne a cikin shekara ta 1986 a kasar Morocco, inda sarki Hassan na biyu ya bayar da umarnin hada dukkanin karatukan kur’ani mai tsarki da marigayi Abdulbasit ya yi.

3936505

Iyalan Abdulbasit Sun Bayar Da Kyautar Kasusuwan Tilawarsa Ga Rediyon Kur’ani na Masar

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: