IQNA

Maradona Ya Kasance Mai Goyon Bayan Al’ummar Falastinu

23:28 - November 27, 2020
Lambar Labari: 3485406
Tehran (IQNA) Diego Maradona fitaccen dan wasan kwallon kafa mai nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falastinu da ke karkashin zaluncin yahudawan Isra’ila.

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniyan nan kuma dan kasar Argentina Diego Maradona, wanda ya gana da shugaban Falastinawa Mahmud Abbas a wasan cin kofon kwallon kafa na duniya  a 2018 a Moscow, ya rasu a sakamakon matsalar bugun zuciya da ya fuskanta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun dan wasan ya fitar a ranar Laraba, ya ce a ranar ne  fitaccen dan wasan ya mutu bayan ya fuskanci matsalar bugun zuciya yana da shekaru 60 a duniya.

A shekaru talatin zuwa arba’in da suka gabata ne e dai tauraruwar marigayi Maradona din ta fara haskakawa a fagen wasan kwallon kafa musamman a shekarar alif da dari tara da tamanin da shida lokacin da ya jagorancin kungiyar kwallon kafa ta kasarsa wato kasar Argentina wajen lashe kofin duniya na kwallon kafa da aka buga a kasar Mexico.

A kasar Argentina din dai shugaban kasar Alberto Fernandez ya sanar da makokin kwanaki uku a daukacin kasar don jimamin mutuwar Maradonan wanda ake gani a matsayin wani gwarzo a kasar.

A farkon wannan wata ne dai aka yi masa tiyata don cire wani gudan jini da ya mamaye kwakwalwarsa.

مارادونا؛ اسطوره حمایت از فلسطین + فیلم

‘Yan wasan kwallon kafa daban-daban ne dai suke ci gaba da fitar da sakonni nuna alnihin rashin wannan dan wasan wanda yana daga cikin sanannun ‘yan wasan da suka yi suna a duniya a fagen kwallon kafa.

Maradona ya kasance mai tsananin nuna adawa da zaluncin da yahudawan Isra’ila suke yi a kan al’ummar Falastinu har zuwa karshen rayuwarsa.

3937570

 

 

captcha