IQNA

An Bayar Da Shawarar Mayar Da Ofishin Wata Cibiyar Musulmin Faransa Da Aka Rufe Zuwa Amurka

14:54 - December 05, 2020
Lambar Labari: 3485431
Tehran (IQNA) cibiyar musulmin Amurka ta bayar da shawarar mayar da ofishin wata cibiyar musulmi a Faransa da gwamnatin kasar ta rufe, zuwa kasar Amurka.

A cikin bayanin da cibiyar musulmin kasar ta Amurka CAIR ta fitar, ta bayyana cewa, tana bayar da shawara ga cibiyar sanya ido kan kyamar musulmi ta kasar Faransa (Collective Against Islamophobia in France) da gwamnatin kasar ta rufe, da ta tattara dukkanin ayyukanta zuwa kasar Amurka.

Bayani ya ce zai fi kungiyar ta bude ofishinta kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a birnin Washington DC na kasar Amurka maimakon kasar Faransa.

Gwamnatin kasar Faransa dai ta rufe wannan cibiya ta musulmi ne da ke sanya ido kan cin zalun da nuna kyama da ake yi wa musulmi a kasar ta faransa tare da harhada rahotanni kan hakan, inda gwamnatin ta zarge ta cewa tana yada addinin muslunci ne, ba ayyukan kare hakkin bil adama ba.

A cikin ‘yan watannin baya-bayan nan dai gwamnatin Faransa ta dauki matakai daban-daban na takura ma musulmi, har ma da shirin korar wasu daga cikinsu da suka nuna rashin amincewa da zanen batuncin da aka yi a kan manzon Allah, kamar yadda kuma gwamnati ta saka masallatai 80 cikin cibiyoyin musulmi da za ta rufe, da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi.

3939055

 

captcha