IQNA

23:16 - December 06, 2020
Lambar Labari: 3485434
Tehran (IQNA) Iran da Ethiopia suna tattauna hanyoyin da za su bi wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa a fagen ilimi, da kuma yaki da corona.

A zantawar da ta gudana tsakanin tsakanin karamin jakadan Iran a kasar Ethiopia Salman Rostami da kuma jami’an kasar ta Ethiopia a bangaren ilimi, bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama dangane da fagagen da za su iya yin aiki tare a bangarorin bincike na ilimi.

Daga cikin abubuwan da tattaunawar tafi mayar da hankali akwai batun aiki tare wajen yaki da cutar corona, inda za su iya hada karfi da karfe a bangaren samar da kayan aiki na kiwon lafiya a wannan fage.

Sannan kuma sun tattauna batun mahangar addinai na muslunci da kiristanci a kan rayuwa da kuma zamantakewa, da yadda wadannan addinai biyu suke bayar da muhimmanci a bangaren kyautata alaka ta zamantakewa tsakanin ‘yan adam.

Shugaban jami’ar Mecanisos ta kasar Ethiopia da ya halarci zaman taron, ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da zama irin wannan tsakanin tawagar Iran, kuma ya zuwa yanzu an iya cimma abubuwa da dama a wannan fage, inda yanzu haka suke da shirin gudanar da taro wanda masana daga kasashen biyu za su gabatar da bayanai a kan mahangar addinan biyu a kan kyautata alaka ta zamantakewa, da kuma yin aiki tare tsakanin dukkanin ‘yan adam.

3939187

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: