Shafin yada labarai na Stuff ya byar da rahoton cewa, ana shirin gudanar da wani taron baje kolin kur’ani mai tsarki a birnin Nelson na kasar New Zealand a karon farko a wannan birni.
Rahoton yace wannan baje kolin kur’ani mai tsarki an gudanar da shi a birane daban-daban na kasar New Zealand, amma wannan shi ne karon farko a birnin Nelson.
Daya daga cikin manufin gudanar da baje kolin shi ne, gabatar da kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin har Mori, wanda shi ne harshen asali na mutanen New Zealand kafin zuwa turawa a kasar.
Wani malamin addini mai suna Mustenser Qamar shi ne wanda yake jagorantar lamarin baje kolin, wanda kuma ya kwashe tsawon shekaru yana gudanar da ayyuka na addini a kasar.
Malamin ya bayyana cewa, mutane da dama a kasar ba su da masaniya akan addini, amma ta hanyar gudanar da wasu taruka irin wadannan da suke tara jama’a daban-daban, hakan wata dama ce ta yin bayani kan addinin musulunci.
Baya ga haka kuma ya ce suna amsa tambayoyin mutane da suke bukatar sanin wasu abubuwa dangane da addinin muslunci.