IQNA

An Kaddamar Da Layin Dogo Wanda Ya Hada Iran Da Afghanistan

23:13 - December 11, 2020
Lambar Labari: 3485450
Tehran (IQNA) shugabannin Iran da Afghanistan sun kaddamar da layin dogo wanda ya hada kasashen biyu.

shugaban kasar Iran Hassan Rohani da takwaransa na kasar Afghanistan Ashraf Gani suka kaddamar da layin dogo da zai hade Gabashin Iran da Yammacin kasar ta Afghanistan, kuma dukkan shuwagabannin sun yi fata hakan zai kara bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen.

A nasa bangaren shugaban Iran Hassan Rohani ya fadi cewa: kasashen biyu a kowanne lokaci suna da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu don haka aikin shimfida layin dogon zai kara taimaka wa wajen karfafa dankon zumunci tsakaninsu.

Daga karshe shi ma shugaban kasar na Aghanistan Ashraf Gani ya yi marhabin da wannan mataki mai cike da tarihi tare da bayyana shi a matsayin wani mataki babba da zai ciyar da tattalin arzikin kasashen guda biyu.

Layin dogon mai nisan kilo mita dari biyu da ashirin da biyar ya kunshi bangarorin hudu ne wanda yanzu haka aka bude, yayin da kilo mita saba’in da takwas na wannan aiki da ya hada da bangarorin biyu yana bangaren kasar Iran ne yayin da sauran kuma yake cikin kasar Afghanistan.

Kasashen Iran da Afghanistan suna da kyakkayawar alaka a dukkanin bangarori na harkokin tattalin arziki cinikayya, da kuma al’adu da suka hada al’ummomin biyu na tsawon dubban shekaru.

 

3940241

 

captcha