IQNA

Majiyoyin Isra'ila Sun Ce Muhammad Bin Salman Ne Ya Sanya Morocco Ta Kulla Alaka Da Isra'ila

21:41 - December 12, 2020
Lambar Labari: 3485453
Tehran (IQNA) Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce yarima mai jiran gadon Saudiyya ne ya yi tasiri kan Morocco domin ta kulla alaka da Isra’ila.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, jaridar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta bayar da rahoton cewa, tun kimanin shekara guda da ta gabata, aka shirya gudanar da wata tattaunawa tsakanin sarkin Morocco, da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma sakataren harkokin wajen Amurka gami da yariman Saudiyya ami jiran gado Muhammad Bin Salman.

Jaridar ta ce saboda bayanai sun fita ga manema labarai dangane da wannan ganawa tun kafin lokacinta, wannan yasa ganawar ba ta yiwuwa ba, saboda sarkin Morocco na tsoron abin da hakan zai iya haifar masa a cikin gida.

Jaridar ta ce ko shakka babu Muhammad Bin salman mai jiran gadon sarautar Saudiyya shi ne ya yi tasiri a kan sarkin Morocco wajen sanar da kulla alaka da Isar’ila.

Ta kara da cewa wanann ba shi ne na karshe ba, domin kuwa akwai wasu kasashen da Saudiyya take da tasiri a kansu wadanda za su biyo baya, baya ga UAE, Bahrain da kuma Sudan gami da Morocco, daga ciki akwai kasashe irin su Oman, Indonesia, Pakistan, Jibouti da makamantansu.

Manufar hakan dai ita ce sanya kasashen musulmi da na larabawa su sanar da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, kafin daga bisa ita kuma masarautar saudiyya ta fito ta bayyana sanarwata, domin sauran kasashe su zame mata kariya daga martani da sukar da za ta fuskata daga al’ummomin musulmi kan haka.

3940459

 

captcha