Musulmin kasar Myanmar wadada su ne marassa rinjayea kasar wadda akasarin mutanenta mabiya addinin Buda ne, suna bayar ad gudunmawa wajen yaki da cutar corona.
Wasu gungun musulmin kasar ta Myanmar ne suke bayar da dukkanin lokacinsu wajen hada karfi da sauran bangarori na kiwon lafiya a kasar, domin taimaka ma jama'a wajen yaki da cutar corona, da hakan ya hada da daukar marassa lafiya da kai su asibitoci da kuma kula da su.
Idan ba manta ba dai musulmin kasar Myanmar suna fuskantar wariya da ake nuan musu saboda addininsu, inda aka kashe dubbai daga cikinsu da kuma mayar da wasu dubban daruruwa 'yan gudun hijira a kasashe makwabta.
3940907