Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Umar Makki dan shekaru 6 da haihuwa daga lardin Alsharkiyya na kasar Masar, shi ne mafi karancin shekaru a kungiyar makaranta da mahardata ta kasar.
Duk da cewa Umar Makki karamin yaro ne, amma kuma a lokaci dabi’unsa na manya ne, ta fuskacin mu’amalarsa, maganganunsa, hatta yadda yake da sakin fuska da karbar jama’a da girmama su, baya ga haka kuma ga shi mahardacin kur’ani mai tsarki.
Umar Makki da kuma kanwarsa Nur Makki ‘yar shekaru hudu da haihuwa, Allah ya yi musu baiwa ta karatu da kuma harder kur’ani mai tsarki.
Saboda kwazonsa da kuma baiwa da Allah ya yi masa a dukkanin bangarori na karatu da kuma hardar kur’ani, wannan ya sanya babbar kungiyar mahardata da makaranta kur’ani ta kasar Masar, ta zabe shi a matsayin daya daga cikin mambobinta.