Marigayi Sheikh Lemu ya rasu yana da shekara 91 a duniya, ya soma karatunsa na addini da na boko a Najeriya inda daga bisani ya tafi Ingila ya kammala Digirinsa na farko a kan African and Oriental Studies a shekarar 1964 a makarantar da a takaice ake kira SAOS.
Ya kwashe galibin rayuwarsa yana koyarwa musamman a fannin Larabci da Ilimin Addinin Musulunci da kuma Hausa ya kuma san wani abu a harshen Farisani.
Kazalika marigayi Sheikh Lemu mutum ne da ya kwashe tsawon rayuwarsa yana kira ga yin masalaha da sassauci a tsakanin al'umma da kuma bayyana ra'ayinsa a kan al'amura ba tare da rufa-rufa ba.
Sheikh Lemu ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kare hakkin mata, haka kuma ya kafa ƙungiyar Da'awa domin yaƙi da tsattsauran ra'ayi.
Baya ga koyarwa, marigayi Lemu ya taka rawa a fannoni da dama, ciki har da fannin shari'ar inda ya rike mukamai daban-daban har da na babban alƙalin Kotun daukaka kara ta Shari'ar Musulunci da ke jihar Naija.
Ya taba zama alkali a Sokoto a tsakanin (1976 – 1977) daga bisani kuma ya zama babban alkalin kotun daukaka kara a jihar Niger a tsakanin (1977 – 1991) kamar yadda kuma ya kasance babban masani a bangaren shari’a da ake dogaro da shi a Najeriya.