Shafin yada labarai na Sahara Media ya bayar da rahoton cewa, Allah ya yi wa Shikhah Maryam Inyas babbar malamar addinin addinin musulunci a kasar Senegal rasuwa bayan kwashe tsawon shekaru tana hidima ga kur'ani da addinin musulunci.
Wannan mata wadda ta shara a fagen yada ilimin kur'ani mai tsarkia kasar Senegal, ita ce kuma ta gina babbar cibiyar kur'ani mafi girma akasar, cibiyar da ta yayae dubban dalibai na cikin kasar Senegal da ma kasashen Afirka da dama.
An haife ta a garin Kaulakha na kasar Senegal a shekara ta 1934, mahaifinta shi ne Sheikh Ibrahim Inyas, babban malamin addinin musulunci, kuma jagoran Faila a darikar Tijjaniya, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada addinin musulunci a kasashen yammacin Afirka.
A cikin shekara ta 2984 ne ta kafa babbar cibiyar addinin musulunci ta Sheikh Ibrahim Inyas a birnin Dakar babban birnin kasar Senegal.