IQNA

Batun Dawowar Annabi Isa (AS) Abu Ne Da Musulmi Da Kirista Suka Yi Imani Da Shi

18:20 - December 29, 2020
Lambar Labari: 3485504
Tehran (IQNA) Malamin kirista Wesam Abu Naser malamin kiristoci a Lebanon ya bayyana cewa, musulmi da kirista sun yi imani da batun dawowar Isa (AS)

A wata zantawa da  kamfanin dillancin labaran iqna, Wesam Abu Naser malamin kiristoci a Lebanon ya bayyana cewa, dukkanin mabiya addinin kirista da musulmi sun yi imani a kan cewa Yesu Almasihu zai dawo karshen zamani, domin yada adalci da aminci a bayan kasa.

Ya ce madaukakin matsayin annabin Isa a wurin musulmi abu ne sananne, kan cewa dukkanin musulmi sun yi iamni da annabi Isa (AS) yana daya daga cikin sharadin iamni a addinin muslunci imani da nnabawan Allah, daga ciki kuwa har da Isa (AS) wanda yana cikin annabawa masu mtsayi a wurin ubangiji da ake kira Ulul Azm.

Dangane da sunayen da kur’ani mai tsarki ya kira annabi Isa da su kuwa, malamin kiristan na Lebanon ya bayyana cewa, kur’ani mai girma ya kira annabi Isa da sunaye daban-daban a cikin ayoyi da surori daban-daban.

Daga ciki akwai inda kur’ani mai girma ya kira annabi Isa (AS) da Ibn Maryam, a wani wurin kuma da Almasihu, sai kuma rasulullah, Nabiyullah, Alwajih, kalimatullah, Almubarak, Abdullah.

Ya ce Almasih Isa dan Maryam a lokacin yahudawa sun san shi da suna Yashu da kuma Yasu’u, wanda ke nufin wanda ya zo daga Allah, amma a cikin addainin muslunci ana kiransa da annabi Isa Almasihu, daya daga daga cikin annabawan Allah mafi girma masu madaukakin matsayin.

Dangane da batun dawowarsa a duniya a karshen zamani kuwa, ya bayyana cewa dukkanin wadanda suka yi imani da shi imani na gaskiya daga cikin mutane, to za su kasance tare da shi, amma kuma ba kowane zai kasance daga cikin mutane ba, sai wadanda suke da tsarkin zuciya, domin kuwa shi mai tsarki ne, saboda haka mutane masu tsarkin ruhi da tsoron Allah ne za su kasance daga cikin mutanensa idan ya dawo.

Ya ce aikin da annabi Isa zai yi idan ya dawo gyara ne, to kuwa babu wadanda za su taya shi wannan aiki sai gyararru daga cikin mutanen da suke  aduniya, wadanda suka gurbata suka nutse a cikin zalunci da sabon Allah, ba su ne masu gyara ba, su ne dai wadanda za a gyara.

Daga karshe ya yi fatan alhairi ga dukkanin al’ummomin duniya dangane da zagayowar lokacin haihuwar annabi Isa (AS) da kuma yin fatan shiga cikin sabuwar shekara miladiyya a cikin alhairi da albarka ga dukkanin al’ummomin duniya, tare da yin fatan Allah ya kawo karshen matsalolin da suka addabi duniya, na cututtuka, da sauran nau’o'in bala’oi kowadanne iri.

 

3943613

 

 

captcha