IQNA

Zarif: Iran Ba Ta Neman Yaki Da Kowa Amma Za Ta Kare Kanta

22:18 - January 01, 2021
Lambar Labari: 3485513
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa kasarsa ba ta neman yaki da kowa, amma za ta kare kanta idan an tsokane ta.

A cikin wani bayani da ya rubuta a shafinsa na twitter, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Amurka tana neman tsokano wani rikici da ba ta shirya masa ba.

Ya ce a maimakon yaki da Corona domin kawo karshenta a cikin Amurka, Donald Trump da wasu ‘yan kanzaginsa suna ta narka biliyoyin daloli wajen tura manyan makamai zuwa yankin gabas ta tsakiya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, sun samu wasu rahotanni na tsaro daga Iraki cewa, Trump yana son ya kirkiro wata hujja domin fakewa da ita wajen kaiwa kasar Iran hari.

Zarif ya ce Iran ba ta neman yaki da kowa, amma kuma za ta kare kanta tare da mayar da mummunan martani a kan duk wanda ya yi gigin tsokanarta da yaki.

3944719

 

 

 

captcha