IQNA

Iran Ta Fara Aikin Tace Sanadarin Uranium Kashi 20% A Shirinta Na Nukiliya

22:18 - January 05, 2021
Lambar Labari: 3485526
Tehran (IQNA) Kakakin fadar shugaban kasar Iran ya bada sanarwar cewa an fara gasa sinadarin uraniyom zuwa kashi 20% a cibiyar makamashin nukliya ta Fordow.

A jiya kakakin fadar shugaban kasar Iran ya bada sanarwan cewa an fara gasa sinadarin uraniyom zuwa kashi 20% a cibiyar makamashin nukliya ta Fordow dake kudancin Tehran.

Kakakin fadar shugaban kasar Iran Ali Rabi'i ya bada sanarwar cewa an fara gasa sinadarin uraniyom zuwa kashi 20% a cibiyar makamashin nukliya ta Fordow dake kudancin Tehran.

Ya kuma kara da cewa an fara aikin ne tare da umurnin shugaban kasa, don yin aiki da kudurin majalisar dokokin kasar wanda ya bukaci hakan, a matsayin daya daga cikin matakan da kasar take dauka don ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

Rabi’i ya kara da cewa za’a fara samun sinadarin uraniyom wanda aka gasa zuwa kashi 20% . Kuma an fara aikin ne baya sanar da hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA da kuma gabatar mata yadda tsarin gasawar zata kasance. Iran ta yi amfani da sabbin na’urorin gasa uraniyom samfurin IR6, UF6 da kuma IR2M a aikin gasawar.

 

3945664

 

captcha