IQNA

Falastinawa Sun Kai Karar Isra’ila Kan Yunkurin Rusa Masallacin Aqsa

22:51 - January 11, 2021
Lambar Labari: 3485545
Tehran (IQNA) Gwamnatin Falastinu ta kai kai Isra’ila a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, kan ci gaba da tona manyan ramuka da take a karkashin masallacin Quds.

A cikin sakon da ma’’aikatar harkokin wajen Falastinu ta aikewa kwamitin tsaro, ta bayyana ci gaba da tonon manyan ramuka a karkashin masallacin aqsa da Isra’ila ke da cewa lamari ne da ya saba wa doka, saboda haka dole ne bangarori na kasa da kasa su taka mata burki.

Bayanin ya ce a halin yanzu Isra’ila ta fafake karkashin masallacin aqsa, kuma  akowane lokaci masallacin zai iya ruftawa, wanda hakan kuma nauyi da ya rataya a kan kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ya dauki mataki kan Isra’ila dangane da wannan lamari.

Ita ma a nata bangarenkungiyar Hamas ta bayyana takaicinta matuka dangane da wannan mummunan aiki da gwamnatin yahudawan Isra’ila take aikatawa, inda ta bayyana cewa manufar hakan ita ce kawar da duk wasu alamu da kuma muhimman wurare na addinin muslunci a cikin Falastinu.

3947126

 

 

 

 

captcha