Tashar Almasirah daga birnin San’a ta bayar da rahoton cewa, kakakin kungiyar Ansarullah Muhammad Abdulsalam, ya kirayi dukkanin kasashen da suka dogara da Trump suka fawwala lamarinsu gare shi, da su dawo cikin taitayinsu, domin kuwa ta Trump ta kare.
Ya ce irin wadannan kasashe da suka mayar da komai nasu ga Amurka, musamman ma shugaban kasar mai barin gado Donald Trump, wanda suka mayar da shi abin dogaro a gare su suka manta da Allah, ya ce lokaci ya yi da za su koma cikin hankalinsu, kuma su kawo karshen kisan kiyashin da suke yi a kan al’ummar msuulmi a Yemen.
Ya ci gaba da cewa, a cikin shekaru 6 da Saudiyya da UAE gami da wasu masu yi musu amshin shata suka kawshe suna kisan mata da kananan yara a Yemen tare da cikakken goyon baya da taimako daga Donald Trump da wasu kasashen turai, babu abin da hakan ya Haifa musu illa zubar mutuncinsu a idon duniya, kuma hisabi na jiransu a gobe kiyama.
Bisa rahotannin da majalisar dinkin duniya gami da kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa suka bayar kan yakin Yemen, rahotannin sun tabbatar da cewa daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar yaki kan kasar Yemen shekaru 6 da suka gabata ya zuwa, ta kashe dubban farraen hula, tare da rusa dubban gidaje da makarantu da asibitoci gami da masallatai da cibiyoyin kasuwanci.
3947702