IQNA

MDD: Saka Wa Kungiyar Ansarullah (Alhuthi) Takunkunmi Da Amurka Ta Yi Yana Tattare Da Hadari

22:48 - January 19, 2021
Lambar Labari: 3485568
Tehran (IQNA) Majalisar dinkin duniya ta bayyana saka kungiyar Ansarullah a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda, zai jefa kasar Yemen cikin wani hali mafi muni.

Kamfanin dillancin labaran sputnik arabic ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake halartar wani zama na kwararru na majalisar dinkin duniya, mai magana da yawun babban sakataren majalisar Stephane Dujarric ya bayyana cewa, matakain da Amurka ta dauka na saka kungiyar Ansarullah a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda hakan yana tattare da babban hadari.

Ya ce, daukar wannan mataki zai kawo cikas ga dukkanin bangarori da majalisar dinkin duniya take gudanar da ayyukanta na jin kai a kasar ta Yemen, kamar yadda hakan kuma zai kassara harkokin kasuwanci na kamfanonin kasashen ketare a Yemen.

Kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce, suna kira da a gagaguta yin nazari kan wannan batu, idan kuma ba hakaba, to duniya za ta shaida matsanancin hali mafi muni da dan adam zai shiga a Yemen, wanda zai zama mafi muni a duniya a cikin shekaru fiye da arba’in da suka gabata.

Bangarori daban-daban na duniya suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wanann mataki da Amurka ta dauka, da hakan ya hada har da kungiyar tarayyar turai, gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya, wadanda suke bayyana matakin da cewa na siyasa ne.

3948571

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :