IQNA

An Gano Wani Masallaci Da Aka Gina Tun Lokacin Sahabban Manzo (SAW) A Yankunan Da Isra’ila Ta Mamaye

22:49 - January 24, 2021
Lambar Labari: 3485584
Tehran (IQNA) an gano wani tsohon masallaci wanda gininsa ke komawa tun lokacin sahabban manzon Allah (SAW) a cikin yankunan Sham da Isra’ila ta mamaye.

Jaridar Times ta bayar da rahoton cewa, an gano wanann masallaci wanda ake sa ran an gina shi ne a cikin shekara ta 635 miladiyya, kuma ana sa ran an gina masallacin ne bisa umarnin daya daga cikin sahabban manzon Allah da ya jagoranci yaki a kasar Sham.

Rahoton jaridar ya  ce masana masu bincike yahudawa daga jami’ar birnin Quds sun gano waannan wuri ne a kusa da koramar garin Tabriyya da ke cikin yankunan larabawa da yahudawan Isra’ila suka mamaye, inda da farko an gano wurin ne ta hanyar samun gishikan tsohon gini, daga baya aka gano bangayensa wadanda sun nutse cikin kasa.

An samu wasu abubuwa na tarihi da suke tabbatar da cewa wurin yana komawa a cikin karni na farko bayan hijirar manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina, da suka hada da wasu kasakai, da kuma wasu kudade da a tarihi ana amfani da su ne a  wancan lokaci.

Masana tarihi dai suna danganta wannan masallacin ne da sahabin manzon Allah Sharhabil bin Hasana, wanda ya jagoranci yaki a yankin Sham, wanda kuma ya gina masallaci a wurin a kusa da koramar Tabriyyah.

Yankin Tabriyyah dai yana cikin yankin Jalil ne da ke kan tuddan Golan na kasar Syria kafin 1967, inda bayan yakin da aka gwabza tsakanin larabawa da yahudawan Isra’ila, tare da taimakon kasashen turai musamman Amurka da Burtaniya, yahudawan Isra’ila suka mamaye yankin har zuwa yanzu.

3949397

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :