IQNA

Babbar Malama Mai Koyar Da Addini A Masar Ta Rasu Bayan Kamuwa Da Corona

22:52 - January 26, 2021
Lambar Labari: 3485590
Tehran (IQNA) Ablah Alkhalawi fitacciyar malamar addinin musulunci a kasar Masar ta rasu bayan kamuwa da cutar corona.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, malama Ablah Alkhalawi ta rasu a ranar Lahadin da ta gabata tana da shekaru 72 a duniya, bayan kamuwa da cutar corona.

Babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar ta fitar da sakon ta’aziyya dangane da rasuwar wannan babbar malamar addini.

Ablah Alkhalawi ta karatun addini a bangaren fikihu da shari’a, inda ta samu digirin digirgir a wannan bangare, kuma tana daga cikin manyan malamai masu koyarwa a jami’ar Azhar.

A tsakanin shekarun 1974 zuwa 1978, ta koyar a jami’oi daban-daban na kasar Saudiyya, kuam tana koyar da mata ilmomin addini a masallacin haramin Makka mai alfarma, amma a karshen shekara ta 1978 ta koma birnin Alkahra da zama baki daya.

Ta kafa babbar cibiyar jin kai da taimakon marasa gaihu mata da kananan yara a kasar Masar da ake kira Baqiyar Salihat, wadda ta shahara wajen gudanar da ayyuka na alhairi a kasar.

 

3949769

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :