IQNA

Firayi Ministan Iraki Ya Sanar Da Halaka Mataimakin Khalifan Daesh

22:51 - January 28, 2021
Lambar Labari: 3485596
Tehran Mustafa Alkazemi firayi ministan Iraki ya sanar da halaka mataimakin khalifan kungiyar ‘yan Daesh a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, firayi ministan Iraki Mustafa Alkazemi ya sanar a yau cewa, dakarun Iraki sun samu nasarar halaka mataimakin khalifan kungiyar ‘yan Daesh.

Mustafa Alkazemi ya ce dakarun Iraki sun samu waann nasara biyo bayan kaddamar da wani farmaki a  maboyar ‘yan ta’addan, inda suka halaka Abu Yaser Al-isawi.

Kazemi ya ci gaba da cewa, dakarun kasar Iraki tare da sauran dukkanin bangarorin tsaro na kasar sun sha alwashin cewa, ba za su taba zama suna kallon Daesh na shirin sake farfadowa a cikin kasarsu ba.

Wannan farmaki da aka fara kaddamarwa a cikin wanann mako ya zo ne biyo bayan harin da kungiyar Daesh ta kaddamar ne a ranar Alhamis da ta gabata, inda ta kashe mutane talatin da biyu tare da jikkata wasu fiye da dari a wani harin kunar bakin wake da wasu ‘yan ta’adda suka kadamar.

Wadanda suka kai harin mutane biyu ne, kuma dukkaninsu ‘yan kasar Saudiyya ne da suka shigo cikin kasar ta barauniyar hanya, wadanda kuma mambobi ne na kungiyar ‘yan ta’addan Daesh.

3950508

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: maboyar ، bangarorin ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :