IQNA

23:47 - February 12, 2021
Lambar Labari: 3485645
Tehran (IQNA) wasu yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma a yau Juma'a.

Shafin yada labarai na Palestine Online ya bayar da rahoton cewa,a ci gaba da daukar matakai na tsokana, a yau wasu yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

A cikin kasa da mako guda, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi kimanin 436 ne suka kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai afamar, da nufin tsokanar musulmi.

A wani labarin kuma wasu yahudawan sun kai wani farmaki a kan yankunan musulmi a gabasin birnin Quds, tare da firgita mazauna yankin.

Baya ga haka kuma sun sauya sunan yankin Jabir da ke gabashin birnin zuwa wani suna na yahudawa, da nufin tabbatar da mamayarsu a kanyankin.

 

3953578

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: