IQNA

Matashi Mai Fasahar Rubutun Larabci A Kasar Masar Ya Samu Izinin Rubuta Cikakken Kwafin Kur’ani

23:47 - February 13, 2021
Lambar Labari: 3485646
Tehran (IQNA) wani matashi dan kasar Masar mai shekaru 19 da haihuwa wanda Allah ya ba shi basira da fasaha ta rubutun larabci ya samu izinin rubutun littafin kur’ani.

Shafin jaridar al-Ahram ya bayar da rahoton cewa, shugaban kungiyar masu fasahar rubutu na kasar Masar Mas’ad Khudair ya bayyana cewa, an bayar da izinin rubuta cikakken kwafin kur’ani da kyakkyawan rubutu ga Abdulkarim Muhammad Marjan.

Marjan ya bayyana cewa, daya daga cikin manyan burukansa shi ne ya samu damar rubuta cikakken kur'ani da rubutu mai kyau wanda za a buga kuma jama'a su amfana da shi.

جوان‌ترین خوشنویس مصری مجوز کتابت قرآن گرفت

Ya ce Abdulkarim matashi ne mai himma matuka wanda ya cancanci hakan da jimawa, wanda a halin yanzu dalibi ne a jami’ar junubul wadi, inda yake karantar harshe da adabin larabci.

جوان‌ترین خوشنویس مصری مجوز کتابت قرآن گرفت

3953693

 

 

 

 

 

captcha