IQNA

Hotunan Muhimman Wurare Na Sojin Isra’ila Da Hizbullah Ta Fitar

16:16 - February 19, 2021
1
Lambar Labari: 3485667
Tehran (IQNA) a daidai lokacin da Isra’ila take barazanar kai wa kasar Lebanon harin soji, kungiyar Hizbullah ta fitar da hotuna na dukkanin muhimma wurare na sojin Isra’ila.

Shafin Al-ahad ya bayar da rahoton cewa,  cikin wani faifan bidiyo da kungiyar Hizbullah ta fitar, ta nuna hotunan muhimman wurare na sojin Isra’ila da suke cikin birane, da suka hada da manyan barikoki na soji.

Faifan bidiyon ya nuna yadda kungiyar ta Hizbullah ta bayar da cikakken bayani ta hanyar hotuna kan muhimman wurare na sojin Isra’ila wadanda aka dauka daga sama.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan jawabin da babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar ne, inda yake gargadin Isra’ila da cewa, idan ta yi shiga wani sabon yaki da kasar Lebanon, a wannan karon za ta fusaknci martani mafi tsanani, wanda ba ta taba gani ba tun daga lokacin da aka samar da ita.

A cikin wani bayaninsa a lokutan baya, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, suna da masaniya  a kan dukkanin muhimman wurare na tsaro da na gwamnatin Isra’ila, kuma a duk lokacin da Isra’ila ta bude yaki da Lebanon, Hizbullah za ta kai hare-hare da wasu makamai na musamman a kan wadannan muhimamn wurare na Isra’ila tare da ragargaza su.

Manyan janar-janar na rundunar sojin Isra’ila dai sun sha nanata cewa, a halin yanzu Isra’ila ba a shirye take ta shiga wani sabon yaki tare da kungiyar Hizbullah ba.

3954834

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Abubakar Ayyuba shuwaki
0
0
Allah ya taimakawa falastinu da sauran ray nanan musulmin duniya baki daya Allah ya kwato mana jagoranmu daga hannun Azzaluman duniya
captcha