IQNA

Afirka Ta Kudu: An Sake Bude Wata Tsohuwar Makabartar Musulmi Da Aka Rufe Ta Fiye Da Shekaru Dari

17:07 - February 20, 2021
Lambar Labari: 3485671
Tehran (IQNA)Mahukunta a kasar Afirka ta kudu sun bayar da izinin sake bude wata makabarta ta musulmi domin bizne gawawwakinsu, sakamako karuwar masu mutuwa saboda corona.

Shafin yada labarai na MSN ya bayar da rahoton cewa, mahukunta a yankin Cape Town tare da kwamitin musulmi na (MJC) na birnin sun cimma matsaya kan bude wata tsohuwar makabarta ta musulmi da ke birnin, domin bizne gawawwakin musulmi da suke mutuwa.

Daya daga cikin mambobin kwamitin musulmi na birnin kuma jami’in kiwon lafiya ya bayyana cewa, an dauki wanann matakin ne bayan cimma matsaya tsakanin gwamnatin Cape Town da kuma musulmin yankin, inda malamai daga cikin musulmi suka bayar da bayani kan halascin yin hakan.

A cikin kowane wata guda, akalla musulmi 150 ke rasa rayukansu a birnin Cape Town, wanda hakan yasa makabartar da suke yin amfani da ita a yanzu ta cika, a kan hakan aka bukaci bude tsohuwar makabartar birnin domin yin amfani da ita.

An fara bizne gawawwakin musulmi ne a wannan makabarta tun a shekara ta 1868, amma daga bisani mahukuntan kasar da suka yi mulkin wariyar launin fata suka rufe wannan makabarta, inda tun daga lokacin fiye da shekaru dari da suka gabata, har yanzu ba a kara bizne wata gawar musulmi a wurin ba.

Ana bizne gawawwaki ne a kasar Afirka ta kudu alokutan aiki, amma an bai wa musulmi damar bizne gawawwakinsu a duk lokacin da suke bukata, bisa koyarwar addininsu.

3954963

 

captcha