IQNA

Shugaban Pakistan Ya Ja Hankalin Faransa Kan Mayar Da Kin Jinin Musulmi Ya Zama Doka

19:54 - February 21, 2021
Lambar Labari: 3485678
Tehran (IQNA) shugaban kasar Pakistan Aref Alawi ya kirayi gwamnatin kasar Faransa da kada ta mayar da kin jinin musulmi ya zama halastacciyar doka a cikin kasarta.

Shafin yada labarai na Donya News ya bayar da rahoton cewa, Aref Alawi shugaban kasar Pakistan ya yi kira ga gwamnatin kasar Faransa da kakkausar murya, a kan cewa kada ta mayar da kin jinin musulmi ya zama halastacciyar doka a cikin kasarta, domin hakan ba zai haifar mata dad a mai ido ba.

A cikin bayanin nasa shugaban kasar ta Pakistan ya bayyana cewa, ko da gwamnatin Faransa ta mayar da dokar takura musulmi da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi, amma kuma  a lokaci guda hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma hakan yana a matsayin tauye hakkokin musulmin kasar ne.

Ya ce wannan mataki na gwamnatin faransa yana tattare da babbar illa ga makomar kasar, wadda kusan kashi goma cikin dari na mutanen kasar musulmi ne, inda hakan zai zama abin kunya ga kasar, a wasu shekaru masu zuwa.

Daga karshe ya kirayi mahukuntan na Faransa da su sake yin tunani kan dokar da suka kafa wadda majalisa ta amince da ita a ranar Talata da ta gabata, wadda ke nufin takura wa musulmi a fadin kasar.

3955211

 

captcha