IQNA

21:35 - February 27, 2021
Lambar Labari: 3485696
Tehran (IQNA) 'yan adawa a Saudiyya da masu rajin kare hakkin dan adama na kasa da kasa sun bukaci shugaban Amurka Joe Biden da ya dau mataki kan yarima Bin Salman.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, wannan dai na zuwa ne bayan rahoton da hukumar leken asirin Amurka ta fitar da ke cewa Bin Salman din ne ke da hannu a kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi.

Idan dai har rahoton ya tabbatar cewa Bin Salman ne ya bada umarnin kashe dan jaridan to kuwa Bin Salman ne ya kamata a kakaba wa takunkumu a cewar kungiyoyin masu fafatukar.

Rahoton sirri da hukumar leken asiri ta kasar Amurka CIA ta tattara dangane da kisan dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, ya nuna cewa yarima Muhammad Bin Salman na da hannu a cikin kisan.

Wannan rahoton da aka hada shi tun lokacin da aka yi wa Jamal Khashoggi kisan gilla, an boye shi tare da kin bayyana shi ga jama’a, bayan da tsohon shugaban Amurka Donald Trump yaki amincewa da yin hakan.

Da dama daga cikin ‘yan majalisar dokokin Amurka sun bukaci sanin wani abu dangane da hakan, amma Trump ya hana fitar da duk wani bayani kan hakikanin abin da ya faru dangane da kisan Khashoggi.

Tun bayan aiwatar da kisan gillar wanda wasu manyan jami’an tsaron gwamnatin Saudiyya suka aikata a cikin ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Istanbul na kasar Turkiya, gwamnatin Saudiyya taki amincewa da faruwar lamarin, inda ta sanar da cewa Jamal Khashoggi ya fita daga cikin ofishin bayan kammala ayyukansa, kamar yadda shi kansa yarima Bin Salman ya furta hakan a wanta zantawa da wata tashar talabijin bayan faruwar lamarin.

To sai dai bayan makonni uku, sakamakon matsin lamba da kuma yadda gwamnatin Turkiya ta fara fitar da wasu bayanan sirri kan yadda aka kashe Jamal Khashggi, hakan yasa ala tilas gwamnatin Saudiyya ta amince da kisan, amma ta dora alhakin hakan ne kawai a kan jami’anta da suka aikata kisan, yayin da ita kuma ta zare hannunta.

Rahoton na CIA ya ce Bin Salman ya amince da kamo Jamal Khashoggi ko kuma kashe shi, yayin da kuma jirage biyu daga cikin jiragen da jami’an tsaron Saudiyya suka yi amfani da su zuwa Turkiya domin kashe Jamal Khashoggi, mallakin Muhammad Bin Salman ne.

Prasow mataimakin Darektan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ya ce hukunta na kuda da Bin Salman ba tare da shi ba kamar kara tunzura shi ne akan ci gaba da aikata muggan laifuka.

A halin da ake ciki dai Saudiyya ta yi watsi da rahoton na Amurka, kan cewa bin Salman ne ke da hannu a kisan dan Jaridan Jamel Khashoggi a ofishin jakadancin kasar dake Turkiyya, duk kuwa da cewa tun daga lokacin faruwar lamarin, dukkanin yatsun tuhuma suna nuni da Bin Salman.

3956514

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: