IQNA

Rahoton IQNA:

Alaka Tsakanin Masarautar Saudiyya Da Sabuwar Gwamnatin Amurka

19:46 - March 01, 2021
Lambar Labari: 3485701
Tehran (IQNA) alaka tsakanin masarautar Al Saud da kuma sabuwar gwamnatin Amurka a karkashin shugabancin Joe Biden, da kuma abubuwan da take kunshe da su.

Tun bayan da sabon shugaban kasar Amurka ya karbi ragamar shugabancin kasar Amurka, ake ganin kamar za a samu canji a cikin salon siyasar Amurka kan gwamnatin kasar Saudiyya, sakamakon irin kalaman da ya rika yi kan gwamnatin da Saudiyya da kuma sukarta, musamman kan batun take hakkokin bil adama.

Irin wadannan kalamai dai Joe Biden ya fara yin su ne tun lokacin yakin neman zabe, inda ya rika sukar gwamnatin Saudiyya kan take hakkokin bil adama, musamman ma masu fafutukar kare hakkokin bil adama, da kuma masu banbancin ra’ayi na siyasa da masarautar Al Saud, ko kuma wadanda take da banbancin mahanga ta fahimta ko akida da su.

Joe ya tsananta sukar gwamnatin Saudiyya ne musamman ma ganin yadda tsohon shugaban kasar ta Amurka yake ba ta kariya da kuma mara baya ga dukkanin abin da take bukata, gami da rufe duk wani abu da zai iya aibanta sunanta a idon duniya, babban misalin hakan shi ne yadda Trump ya tsaya kai da fata domin ganin an rufe batun kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi mai sukar salon siyasar yarima mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman, wanda tun a lokacin shi ne ake tuhuma da hannu a kisan Khashoggi.

تغییر رویکرد آمریکای جو بایدن در مقابل سعودی‌ها با محوریت پرونده خاشقچی

Wani abu da ya kara sanya da dama daga cikin mutane suke zaton cewa za a samu canji a alakar Amurka da Saudiyya shi ne yadda gwamnatin Biden ta fara da bankado batun kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi, da sanya hukumar liken asiri ta kasar Amurka CIA ta fitar da rahoton da ta harhada tun lokacin da aka yi kisan a cikin watan Oktoban 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Tun bayan hada wannan rahoto, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya hana a mika shi ga majalisar dokokin Amurka, tare da hana daukar duk wani mataki na ladabtarwa a kan gwanatin Saudiyya

تغییر رویکرد آمریکای جو بایدن در مقابل سعودی‌ها با محوریت پرونده خاشقچی

Bankado wannan batu da Biden ya yi ‘yan kwanaki bayan karbar ragamar mulkin Amurka, tare da tabbatar da cewa bisa ga rahoton CIA, Bin Salman ne ke da hannu a wannan kisa, wasu na tsammanin cewa Amurka za ta sauya siyasarta dangane da Saudiyya.

Sai dai wadanda suke bin diddigin lamurra na siyasar duniya suna ganin sabanin hakan, domin kuwa a lokacin mulkin Trump ya yi amfani da wannan damar ne a matsayin wani makami na tsorata Saudiyya a bayan fage,tare da tatsar makuden kudade na daruruwan biliyoyin daloli daga gare ta.

Masanan sun yi imanin cewa ko a wannan karon ma abin da zai faru kenan, batun kisan Khashoggi babbar dama  ce wadda shi ma Joe Biden zai yi amfani da ita domin ya tatsi nasa rabon na daruruwan biliyoyin daloli daga gwamnatin Saudiyya, tare da ci gaba da tsorata ta da wanann batu da sauran batutuwa na cin zarafi da take hakkin ‘yan adam a kasar, domin ta ci gaba da zama saniyar tatsa kamar yadda Donald ya kira masarautar ta Saudiyya.

تغییر رویکرد آمریکای جو بایدن در مقابل سعودی‌ها با محوریت پرونده خاشقچی

Babu wani mataki na ladabtarwa ko hukuntawa da sabuwar gwamnatin Amurka karkashin Joe Biden za ta dauka kan yarima Bin Salman, matakin dai bai wuce abin da Biden ya fada ba, na cewa zai yi mu’amala ne kai tsaye tare da sarki Salman Bin Abdulaziz maimakon Muhammad Bin Salman, sabanin Trump wanda ya kasance ya mayar da Bin Salman tamkar shi ne sarkin, domin kuwa dukiyar kasar Saudiyya tana a hannunsa ne, yafi sauki a tatsa daga gare shi kai tsaye.

Haka nan kuma masana suna ganin cewa, Biden zai yi amfani da Saudiyya kamar yadda Trump ya yi, wajen ci gaba da sanya ta, ta zama mai jawo hankulan kasashen larabawa da na musulmi domin su kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, domin kuwa babu wata kasa a tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya da za ta iya kare manufofin siyasar Amurka da na Isra’ila tare da aiwatar da su a acikin yankin kamar Saudiyya.

A kan haka masana harkokin siyasar kasa da kasa suna ganin cewa, babu wani canji a alakar Amurka da Saudiyya, domin kuwa Amurka ba za ta iya wadatuwa daga barin Saudiyya ba, saboda kudin da take tatsa wadanda babu wata kasa a duniya da za ta iya tatsar irin wadannan kudaden daga gare ta kamar Saudiyya, kamar yadda ita ma Saudiyya ba ta iya wadatuwa daga barin Amurka ba, saboda tunanin da sarakunan kasar suke da shi kan cewa, Amurka ce kawai za ta iya kare su tare da lamunce musu ci gaba da mulki, kamar yadda shi kansa Trump ya sha nanata cewa, in ba don Amurka da kariyarta ba, to da sarkin Saudiyya ba zai iya yin mako biyu a kan kujerar mulki ba.

 

3956713

 

captcha