IQNA

14:55 - March 02, 2021
Lambar Labari: 3485704
Tehran (IQNA) matar da Jamal Khashoggi ke shirin aura kafin yi masa kisan gilla a Turkiya ta bukaci da a gaggauta gurfanar da Bin Salman a gaban shari’a.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Khadijah Genghiz matar da dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi ke shirin aura kafin yi masa kisan gilla a Turkiya ta bukaci da a gaggauta gurfanar da Bin Salman a gaban shari’a domin ya fuskanci hukunacin abin da ya aikata.

Ta c eta yi na’am da rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar kan batun kisan Jamal Khashoggi, da kuma kiran da babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai gudanar da bincike ta yi, na yi adalci wajen gurfanar da Bin Salman a gaban kotu.

Ta ce duk wani mataki da za a dauka a kansu tare da kubutar da yarima Bin Salman daga fuskantar hukuncin kisan kai ba adalci ba ne ga Jamal Khashoggi.

A kan haka ta ce rahoton baya-bayan nan na hukumar leken asirin asiri ta Amurka, yana kara tabbatar da gaskiyar lamarin ne, a kan haka babu wani dalili na yin zagaye-zagaye domin kin gurfanar da Birn Salman a gaban kuliya.

 

3957062

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: