IQNA

22:02 - March 05, 2021
Lambar Labari: 3485715
Tehran (IQNA) a yau ne babban jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya fara ziyarar aiki a kasar Iraki.

Tashar Al-alam ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da ya isa fadar shugaban kasar Iraki a yau, Paparoma ya samu tarbe daga shugaban kasar Barham Saleh, inda suka tattauna muhimman lamurra da suka shafi muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai da ma ‘yan adam baki daya.

Dangane da yanayin da kiristocin kasar Iraki suka samu kansu a baya a  lokacin da ‘yan ta’adda suka addabi kasar Iraki, Paparoma ya bayyana abin da ya faru da cewa abin bakin ciki ne matuka.

Ya ce dole ne mu yi amfani da koyarwar da takea  cikin addinanmu na musulunci da kirastanci, wadda koyarwa ce ta zaman lafiya da kaunar juna, da kuma girmama fahimtar juna, wanda wannan shi ne asasi na zaman lafiya a cikin zamantakewar al’umma.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Iraki ya bayyana ziyarar ta Paparoma a Iraki da cewa, ziyara ce ta tarihi, wadda take dauke da sakonni masu yawa ga al’ummomin Iraki, musulmi da kirista, da ma dukkanin al’ummomin gabas ta tsakiya da na duniya baki daya.

A matakin farko dai babban sakon wannan ziyara shi ne ‘yan uwantaka tsakanin da ‘yan adamtaka tsakanin dukkanin mabiya addinai, musamman kiristoci da musulmi.

3957713

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: