IQNA

16:48 - March 08, 2021
Lambar Labari: 3485726
Tehran (IQNA) ziyarar Paparoma Francis a kasar Iraki dai ta dauki hankula matuka fiye da sauran ziyarori da ya kai a kasashen duniya.

Tun a  ranar Juma’a da ta gabata ce dai jagoran mabiya addinin kirsita na darikar Katolika Paparoma Francis ya fara gudanar da ziyara ta kwanaki uku a kasar Iraki.

Wannan ziyara tasa ta zo ne a  daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli a duniya, musamman ma dai matsalar ta cutar corona, wadda ta addabi duniya baki daya, wanda kuma duk da haka ya jaddada cewa zai gudanar da wannan ziyara kamarv yadda aka tsara.

Tun daga farko dai ya bayyana cewa zai gana da babban malamin addini na kasar ta Iraki Ayatollah Sistani, da kuma jagorori na mabiya addinin kirista da sauran bangarori na al’ummomi da kabilu na kasar.

Bayan isarsa birnin Bagadaza a ranar Juma’a da ta gabata, Paparoma ya samu gagarumar tarba daga gwamnatin Iraki, inda Firayi minsitan kasar Mustafa Alkazimi ya tarbe a babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza.

Bayan nan kuma Paparoma ya ziyarci fadar shugaban kasar Irakia  cikin birn Bagadaza, inda a nan ma ya samu kyakkayawar tarba ta ban girma daga shugaban kasar Iraki Barham Saleh, banyan nan kuma sun tattauna kan batutuwa da dama, da suka hada da kara karfafa alaka tsakanin gwamnatin Iraki da fadar Vatican.

پاپ عراق را ترک کرد / حضور پاپ در عراق محصول تلاش‌های شهید المهندس است

Haka nan kuma bangarorin biyu sun tabo batun halin da mabiya addinin kirista suke ciki a Iraki, inda shugaban kasar ta Iraki ya bayyana ma Paparoma cewa, mabiya addinin kirista a Iraki, bangare ne na al’ummar kasar da ba  za a taba raba su ba, domin kuwa Iraki kasarsu ce, kuma su babban bangare ne na al’ummar kasar, wadanda suke da hakkoki kamar kowane dan kasa ta fuskar addini da kuma ‘yanci na siyasa da zamantakewa.

Shi ma a nasa bangaren paparoma ya jinjina wa gwamnatin Iraki, kan yadda take baiwa mabiya addinin kirista  a kasar hakkokinsu da kuma ba su kula, kamar yadda ya jaddada wajabcin ci gaba da kara samun irin wannan fahimta da kuma taimakekeniya tsakanin dukaknin bangarori na addinai.

پاپ عراق را ترک کرد / حضور پاپ در عراق محصول تلاش‌های شهید المهندس است

Bayan nan kuma Paparoma ya gana da shugaban majalisar dokokin Iraki Muhammad Alhalbusi, kamar yadda ya gana da manyan malaman addinin kirsita a birnin Bagadaza, tare da halartar wasu daga cikin majami’oin birnin.

Sannan kuma Paparoma ya yi wani abu wanda ya dauki hankula matuka a lokacin da yake cikin birnin Bagadaza, inda ya girmama dakarun sa kai na al’ummar Iraki da suka fattataki ‘yan ta’addan Daesh, wato dakarun Hashd Al-shaabi, inda ya bayar da kyautar casbinsa da yake amfani da shi a tarukan addini a fadar Vatican, ga daya daga cikin kwamandojin rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Iraki wato Rayyan Al-kildani.

Wannan kwamanda shi ma mabiyin addinin kirsita ne, wanda shi da wasu kiristoci suka shiga a cikin musulmi domin kare kasarsu da al’ummarsu, wanda hakan hakan ke nuni da goyon bayan Paparoma ga ayyukan dakarun sa kai na al’ummar Iraki, tare da karfafa mabiya addinin kirista na kasar da su hada kai da musulmi domin yin aiki tare, saboda ci gaban al’ummarsu da kasarsu.

پاپ عراق را ترک کرد / حضور پاپ در عراق محصول تلاش‌های شهید المهندس است

Wani abu kuma wanda shi ne yafi daukar hankula a ziyarar ta paparoma Francis a Iraki, shi ne ganawarsa da babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani, inda Paparoma ya kai masa ziyara har gidansa da ke birnin Najaf, kuma suka tattauna muhimamn batutuwa da suke da alaka da muhimamncin samun fahimtar juna da zaman lafiya da girmama fahimta tsakanin dukaknin mabiya addinai, musamman ma kirista da musulmi, kamar yadda suka bayyana hakan da cewa shi ne ya kamata ya zama a takanin dukkanin mutanen duniya.

Paparoma ya yi godiya ta musamman ga Ayatollah Sistani, dangane da ya bayar, ta yin yekuwa domin kubutar da kasar Iraki, a lokacin da mayakan ‘yan ta’adda na Daesh suka shigo kasar da nufin mamaye ta, inda suka fara yanka musulmi da kirista da ma duk wani wanda baya a cikinsu.

Wannan fatawar ta Ayatollah siistani ce ta bayar da damar kafa rundunar sa kai wadda ta kare musulmi da kirista, inda wannan rundunar ce ta kubutar da dubban kirisrtoci daga yankan rago a  hannun ‘yan ta’addan daesh, kamar yadda kuma ta kubutar da manyan majami’o na mabiya addinin kirsista na tarihi da suke a kasar Iraki, kamar yadda ta kubutar da masallatai da cibiyoyin addini da kuma rayukan jama’a ba tare da banbanci ba.

Bayan nan kuma Paparoma ya kai ziyara a babbar majamii’ar birnin Mausil wadda aka gina ta tun kusan shekaru 2000 da suka gabata, kamar yadda ya ziyarci garin Ur inda aka haifi annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda yake a lardin Nasiriyya da ke kudancin kaar ta Iraki.

پاپ عراق را ترک کرد / حضور پاپ در عراق محصول تلاش‌های شهید المهندس است

Daga nan kuma Paparoma ya ziyarci yankin Kurdestan na Iraki, inda ya gana da bangarori daban-daban na al’ummomin wannan yanki, daga karshe kuma ya koma birnin Bagadaza, inda a jiya Litinin ya kuma ya bar birnin Bagadaza zuwa fadar Vatican.

A wani bayani da ya yi a yau fadar Vatican bayan komawarsa gida daga ziyarar da ya gudanar a kasar ta Iraki, jagoran mabiya addinin kirsita na darikar Katolika Paparoma Francis ya bayyana farin cikinsa maras misiltuwa dangane da yadda ziyarar ta kasance.

Ya bayyana wanann ziyara da cewa ta tarihi ce, domin kuwa ita ce irinta ta farko da wani jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika na duniya ya kai a kasar.

3958318

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: