IQNA

Matsayar Ayatollah Sistani A Ganawarsa Da Paparoma Ita Ce Kin Yarda Da Zalunci A Kan Al'ummomin Duniya

23:46 - March 11, 2021
1
Lambar Labari: 3485736
Tehran (IQNA) a ganawar da ta gudana tsakanin Ayatollah Sistani da Paparoma Francis Ayatollah Sistani ya tabbatar da matsayarsa ta kin amincewa da zalunci a kan al'ummomin duniya.

Ayatollah Sistani ya tabbatar da matsayarsa ta kin amincewa da zalunci da danniya da mamaya da danne hakkoki na al'ummomin duniya, a ganawarsa da Paparoma Francis.

Bayan ziyarar da jagoran mabiya addinin kirista na darikar katolika Paparoma ya kai kasar Iraki, masana a kan harkoki na siyasar kasa da kasa suna ganin cewa, wannan ita ce ziyara irin ta ta farko da wani babban jagoran kiristoci ya kai wata kasar musulmi wadda ta yi nasara a shekarun baya-bayan nan.

Babban abin da yafi daukar hankalia  ziyarar ta Paparoma dai shi ne ganawarsa da babban malamin addinin musulunci na kasar Iraki, wanda yake da babban tasiri a kasar da kuma mazhabar shi'a a duniya.

Babban abin da Ayatollah Sistani ya bayyana a ganawarsa da Paparoma shi ne, dole ne adalci ya zama birbishin komai, a daina zalunci da danne al'ummomi raunana a duniya, samar da yayanayi na fahimtar juna sakanin dukkanin mabiya addinai.

3959115

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 1
Ba A Iya Watsa Shi: 0
buhari ali
0
0
ameeeen ya allah
captcha