IQNA

1:32 - March 12, 2021
Lambar Labari: 3485737
Tehran (IQNA) an sake bude masallatai a kasar Bahrain bayan rufe su na tsawon lokaci.

Kamfanin dillancin labaran BNA ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini  a kasar Bahrain tasanar da cewa, bayan rufe masallatai na tsawon lokaci a kasar an sake bude su a yau a fadin kasar.

Bayanin ya ce mataki dakatar da sallolin Juma'a yana nan daram, amma za a rika gudanar da salloli biyar na rana.

An dauki matakin ne bayan yin shawara da dukkanin bangarori na malaman kasar, da suka hada da 'yan shi'a wadanda su ne suka yawa a kasar, da kuma 'yan sunnah.

Duk da bude masallatan, matakan kula da lafiyar jama'a na nan kamar yadda aka saba, za a ci gaba da yin aiki da su.

3959080

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dukkanin bangarori ، malaman kasar ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: