IQNA

2:15 - March 12, 2021
Lambar Labari: 3485739
Tehran (IQNA) majiyoyin gwamnatin kasar Rasha sun sanar da cewa, wata tawagar 'yan majalisa na kungiyar Hizbullah ta Lebanon za ta ziyarci birnin Moscow.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin kasar Rasha sun sanar da cewa, wata tawagar 'yan majalisar dokokin kasar Lebanon daga bangaren kungiyar Hizbullah za ta ziyarci birnin Moscow a cikin wannan mako.

Bayanin ya ce tawagar karkashin jagoran Muhammad Raad shugaban gungun 'yan majalisa na Hizbullah a majalisar dokokin Lebanon.

A yayin ziyar tawagar ta Hizbullah za ta gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Rasha, da suka hada da ministan harkokin waje Sergey Lavrov, da kuma mataimakinsa Mikhail Bogdanov, gami da shugaban kwamitin kula da lamurran siyasar kasa da kasa a majalisar dokokin kasar Rasha.

Bangarorin za su tattauna kan batutuwa da suka shafi yanayin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun kasar Syria.

3959117

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: