IQNA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha Ta Fitar Da Bayani Kan Ganawar Jami'an Rasha Da Tawaggar Hizbullah A Moscow

23:50 - March 16, 2021
Lambar Labari: 3485748
Tehran (IQNA) ma'ikatar harkokin wajen Rasha ta fitar da bayani kan ganawar da aka yi tsakanin jami'an gwamnatin Rasha da tawagar Hizbullah

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, ma'ikatar harkokin wajen Rasha ta fitar da bayani kan ganawar da aka yi tsakanin jami'an gwamnatin Rasha da tawagar Hizbullah a birnin Moscow.

Bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ya ce, an gudanar da tattaunawa tsakanin manyan jami'an gwamnatin Rasha da kuma tawagar kungiyar Hizbulla, inda aka tattauna batutuwa da dama.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey ne ya jagoranci tawagar gwamnatin Rasha a wannan tattaunawa, yayin da Muhammad ra'ad shugaban bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon ya jagoranci tawagar Hizbullah.

Bangarorin biyu sun tattauna kan muhimmancin yin aiki tare a tsakanin dukkanin bangarori domin samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda suka tattauna batun halin da ake ciki Syria da Lebanon.

Rasha ta jadda cewa, dole ne bangarorin siyasar Lebanon su warware matsalolinsu ba tare da shigar shugula daga wasu bangarori na kasashen ketare ba.

 

 

3959968

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tawagar hizbullah birnin Moscow har
captcha