IQNA

23:34 - March 27, 2021
Lambar Labari: 3485767
Tehran (IQNA) za a gina manyan ciyoyin musulunci guda 10 a kasar Saliyo

Kamfanin dillancin labaran All Africa ya bayar da rahoton cewa, baya ga gina cibiyoyin musulunci na zamani guda 10, gamayyar kungiyoyin matasa musulmi a kasar Saliyo na gina rijiyoyon burtsatse guda 120 a fadin kasar, sannan kuma sun samar da ayyukan yi ga matasa fiye da dubu 8000.

Dr. Hamid Ahmad Kanneh shugaban bangaren gudanarwa na wannan cibiya ya bayyana cewa, cibiyoyin da za a gina za su kunshi masallaci da kuma makaranta gami da wuraren alwalla da kuma cibiyar kiwon lafiya gami da gidan limamin da zai rika jagorantar salla da yi ma mutane wa’azi da fadakarwa.

An kafa cibiyar matasa musulmi ta kasar saliyo wato The International Islamic Youth League a cikin shekara ta 1991, sannan kuma tun daga lokacin tana gudanar da ayyukan taimako da bayar da tallafi ga mabukata, sannan kuma kungiyar tana samun taimako daga wasu cibiyoyi daga kasashen Asia da kuma na larabawa a yanking abas ta tsakiya.

 

3961263

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: