Shafin yada labarai na Tribune online ya bayar da rahoton cewa, an kawo karshen gasar kur’ani ta kasa karo na talatin da biyar a tarayyar Najeriya, taron da aka gudanar a jihar Kano.
Nasiru Gawuna mataimakin gwamnan jihar Kano ya bayyana a wajen taron rufe gasar cewa, wannan taron gasar kur’ani ya samu halartar makaranta da mahardata mata da maza, 180 daga cikinsu maza ne, 190 kuma mata ne.
Haka nan kuma ya bayyana cewa dukkanin mahalrta taron sun fito daga jihohi 36 na fadin kasar, inda suka kara da juna, kuma kowanensu ya nuna kwazonsa.
A wannan gasa Muhammad Awwal Gusau daga Jihar Zamfara shi ne ya zo na daya, sai kuma a bangaren mata Nusaiba Shu’abu Ahmad ce daga jiha Kano ta zo ta daya.
bangaren