IQNA

An Yi Gargadi Dangane Da Hadarin Da Ke Fuskantar Masallacin Quds Mai Alfarma Daga Yahudawa

17:33 - April 04, 2021
Lambar Labari: 3485783
Tehran (IQNA) an yi gargadi dangane da irin hadarin da masallacin quds mai alfarma yake fuskanta daga yahudawa masu tsatsauran ra’ayi.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya nakalto daga daya daga cikin mambobin kwamitin kula da masallacin quds Nahadi Al-halwani yana cewa, akwai babbar barazana dangane da irin hadarin da masallacin quds mai alfarma yake fuskanta daga yahudawan sahyuniya.

Ya ce yahudawan suna shirin gudanar da wani babban taro da suke kira ranar idin yahudawa, wanda zai kama a wannan shekara a ranar 28 ga watan Ramadan, wanda yahudawan za su yi gangami a cikin masallacin aqsa tare da keta alfarmarsa.

Al-halwani ya ce, yahudawan suna niyyar raba masallacin quds bangaren gabashinsa da kuma yammaci, inda suke da nufin mamaye gabashin masallacin tare da raba shi da kofar babu rahma da ke yammacinsa.

Ya ce yahudawan suna da nufin gina wurin bauta na haikal a cikin masallain aqsa daga yankin gabacinsa, kuma har yanzu suna nan kan wannan niyya tasu, kuma suna samun goyon baya daga gwamnatinsu da ma gwamnatocin da ke mara musu baya, daga cikin har da wasu munafukai daga cikin gwamnatocin larabawa da sarakunansu.

 

3962294

 

 

 

 

captcha