IQNA

Babbar Gasar Kur’ani Ta Kasa Na Ci Gaba Da Gudana A Mauritania

12:12 - April 06, 2021
Lambar Labari: 3485788
Tehran (IQNA) ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa wadda ta kebanci yara a kasar Mauritaniya.

Shafin yada labarai na al-akhbar ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa wadda ta kebanci yara a kasar Mauritaniya, wadda cibiyar kula da kanan yara da kuma cibiyar Ubai Bin Ka’ab suke dauki nauyin shiryawa.

Wannan dais hi ne karo na hudu da ake gudanar da wannan gasar kur’ani a kowace shekara, sannan kuma ana gudanar da gasar a dukkanin matakai ne na hardar kur’ani, wadda ta kunshi dalibai 250 daga dukkanin sannan kasar.

A halin yanzu dai ana cikin mataki rukuni-rukuni ne, kafin kaiwa ga mataki na kusa da na karshe da kuam matakin karshen gasar baki daya.

Bisa ga bayanin masu kula da gasar, za a kamala ta ne a cikin watan Ramadan mai alfarma, inda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazoa  dukkanin matakai.

3962639

 

 

 

 

captcha