IQNA

Kwafin Kur'ani Da Aka Rubuta Lokacin Khalifa Usman Bin Affan A Dakin Karatu Na Azhar

22:54 - April 20, 2021
Lambar Labari: 3485831
Tehran (IQNA) an mika wa dakin karatu na cibiyar Azhar ta kasar Masar kwafin kur'ani da aka rubuta a lokacin Khalifa Usaman Bin Affan.

Sheikh Ahmad Tayyib shugaban cibiyar azhar, ya mika wa dakin karatu na cibiyar Azhar ta kasar Masar kwafin kur'ani da aka rubuta a lokacin Khalifa Usaman Bin Affan, wanda aka yi kwafinsa.

Wannan kur'ani dai an dauki kwafinsa ne a kan wasu takardu, wadanda suke dauke da sabon rubutu na zamani da yake dauke da wasulla da kuma digo a kan bakaken larabci.

Fadin kur'ani da tsawonsa zai kai C30 da kuma C40, sannan kowane shafi yana dauke da layukan rubutu 18 na rubutun ayoyi.

Dakin karatu na cibiyar Azhar yana yankin Aqsar ne a  yammacin birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, wanda aka bude shi da littafai dubu 17, amma daga bisani an kara adadin yawan litatfan.

کتابخانه الازهر صاحب نسخه قرآن عثمانی شد

کتابخانه الازهر صاحب نسخه قرآن عثمانی شد

3965779

 

captcha