IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani Ta Matasa Makafi A Kasar Tanzania

18:58 - April 21, 2021
Lambar Labari: 3485833
Tehran (IQNA) cibiyar Aisha Surur da ke daukar nauyin ayyuka da suka shafi kur'ani ta dauki nauyin shirya gasar kur'ani ta matasa makafi.

A rahoton kamfanin dillnacin labaran iqna, a jiya ne aka fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta matasa makafi a birnin Dar salam na kasar Tanzania, inda makaranta da mahardata 68 mata da maza suke halartar gasar.

Shubar wannan cibiyar Aisha Surur da kanta ce ta shirya gasar, kuma take halartar wurin, tare da baki da aka gayyata da suka hada da jami'an gwamnati, malaman addini, wakilan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi, gami da wasu jakadu daga cikin jakadun kasashen musulmi a kasar ta Tanzania.

Ta bayyana cewa, manufar shirya wannan gasa ta kur'ani ta kunshi matsa makafi zalla ita ce, kara karfafa gwiwarsu a kan lamarin da ya shafi kur'ani mai tsarki.

Bayan kammala wannan gasa dai za a bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadnda suka fi nuna kwazo.

 

3966001

 

 

 

captcha