IQNA

Shugaba Rauhani: Abin Da Muke Bukata Shi Ne Aiwatar da Yarjejeniyar Nukiliya Kamar Yadda Take

19:12 - April 21, 2021
Lambar Labari: 3485834
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani ya ce hanya daya ta warware batun shirin makamashin Nukiyar Iran, shi ne aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kamar yadda take

A cikin wani bayaninsa da ya gabatar a yau a zaman taron jami'an bangaren zartarwa, shugaban kasar ta Iran ya ce; Kowa ya san cewa hanya daya ta warware batun shirin makamashin Nukiyar Iran, shi ne aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kamar yadda take ba tare da ragi ko kari ba.

Shugaba Hassan Rauhani wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron majalisar minstoci a yau Laraba, ya ci gaba da cewa; Iran ba ta son wani kari, amma anan gaba za ta gabatar da wasu bukatunta da su ka hada da asarar biliyoyin dalolin da aka sa ta yi saboda takunkumin da aka kakaba mata a cikin shekaru hudu.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar Iran ya kunshi yin ishara da ci gaban da ake samu a tattaunawar da ake yi a yanzu a Vienna a tsakanin Iran din da sauran bangaren wadanda su ke cikin yarjejeniyar.

Yanzu haka dai ana gudanar da tattaunawa tsakanin Iran da sauran bangarorin yarjejeniyar nukiliya a birnin Vienna na kasar Austria, inda ake kokarin ganin an lalubo hanyoyin warware dukkanin matsalolin da suka taso dangane da yarjejeniyar.

 

3966219

 

captcha