IQNA

17:44 - April 22, 2021
Lambar Labari: 3485836
Tehran (IQNA) an raba kayayyakin kiwon lafiya ga masu gudanar da ayyukan ibadar Umrah a masallacin haramin Makka mai alfarma.

Shafin jaridar The Gulf News ya bayar da rahoton cewa, hukumar da ke  kula da harkokin hajji da Umrah a kasar Saudiyya ta sanar da cewa, domin kaucewa kamuwa da cutar corona ko yada ta a tsakanin masu gudanar da ayyukan ibada na Umrah, an tanadi kayayyakin kiwon lafiya na musamman, wadanda ake rarraba su ga dukaknin masu gudanar da wadannan ayyukan na ibada a cikin wannan wata.

Bayanin ya ce, ana raba kayan ne ga masu ayyukan Umrah bayan da aka hada su a cikin wata karamar jaka, daga cikin kayayyakin akwai sanadarai masu kashe kwayoyin cuta, da kuma lema gami da dardumar salla guda daya, sai kuma takunkuman rufe baki da hanci.

Haka na kuma ana kara tsananta daukar matakai na tabbatar da cewa an bayar da tazara tsakanin mutane a cikin masallacin harami a lokacin da salla da kuma lokutan dawafi.

A baya-bayan nan dai mahukuntan Saudiyya sun sassauta dokar shiga masallacin harami, inda yanzu aka kara yawan adadin mutanen da za su iya shiga wurin a lokaci guda.

3966479

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: