IQNA

Masallacin Ahmad Al-fuli Na Daga Cikin Masallatai Na Tarihi A Kasar Masar

18:13 - April 22, 2021
Lambar Labari: 3485837
Tehran (IQNA) masallacin Ahmad Al-fuli na daga cikin masallatai na tarihi a kasar Masar da ke jan hankula masu yawon bude ido a kasar.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, lardin Alminya na daga cikin larduna da suke da wuraren tarihi a kasar Masar, da hakan ya hada da wurare da sarakunan fir’aunoni suka gina tun fiye da shekaru dubu uku da suka gabata.

Baya ga haka kuma akwai wurare wadanda na tarihi ne da suke da alaka da tarihin addinin muslunci a kasar, wasu daga cikin wuraren an gina su ne ‘yan shekaru bayan zuwan musulunci a Masar, wasu kuma daruruwan shekaru bayan zuwan muslunci a kasar.

Masallacin Ahmad Al-fuli na daga cikin masallatai na tarihi a kasar Masar da ke jan hankula masu yawon bude ido a kasar matuka, duk kuwa da cewa an gina masallacin ne kasa da shekaru dari biyar da suka gabata.

Ana danganta masallacin ne da Ahmad Al-fuli Ali Bin Muhammad bin Ali Al-yamani Al-Misri, daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Masar, wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kara karfafa cibiyar Azhar a kasar.

آشنایی با مسجد احمد الفولی، از مساجد باستانی مصر + عکس  
 
آشنایی با مسجد احمد الفولی، از مساجد باستانی مصر + عکس  
 
آشنایی با مسجد احمد الفولی، از مساجد باستانی مصر + عکس  
 
آشنایی با مسجد احمد الفولی، از مساجد باستانی مصر + عکس  
 
آشنایی با مسجد احمد الفولی، از مساجد باستانی مصر + عکس  

3966031

 

captcha