IQNA

Natsuwar Ruhi Tana Bude Kofofin Fahimtar Ma'anonin Kur'ani Mai Tsarki

23:20 - April 27, 2021
Lambar Labari: 3485851
Tehran (IQNA) Sayyid Hashem Musawi shugaban cibiyar musulunci ta birnin Landan ya bayyana natsuwar ruhi a matsayin daya daga cikin hanyoyi da ke taimakawa wajen fahimtar ma'anonin kur'aani.

A cikin wani jawabinsa da ya gabatar, Sayyid Hashem Musawi shugaban cibiyar musulunci ta birnin Landan na kasar Burtaniya ya bayyana cewa, natsuwar ruhi na daga cikin muhimman hanyoyin da ke taimaka wa mumuni wajen fahimtar ma'anonin kur'aani kur'ani mai tsarki.

Ya ce lokacin azumin watan yana daga cikin lokuta da musulmi yake samun natsuwar ruhi, saboda ladabtar da jikinsa da yake yi da kuma tarbiyantar da shi a kan bautar Allah fiye da kowane lokaci.

Ya kara da cewa,a  duk lokacin da musulmi ya yi amfani da damar da ya samu a cikin wannan lokaci mai albarka wajen kara samun kusanci da Allah, to ruhinsa zai kara samun natsuwa, kuma kofofin fahimta za su kara bude masa, daga ciki kuwa da fahimtar ma'anoni na zancen Allah madaukakin sarki.

 

3966177

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: birnin Landan cibiyar musulunci
captcha