IQNA

Kada Mu Bar Damar Tuba Da Istigfari A Dararen Lailatul Qadr

23:29 - May 01, 2021
Lambar Labari: 3485864
Tehran (IQNA) babban malami a cibiyar ilimi ta Hauza da ke birnin Qom a Iran ya bayyana daren Lailatul Qadr a matsayin babbar dama ta tuba zuwa ga Allah daga zunubbanmu.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna Ayatollah Sayyid Muhammad Gharawi ya bayyana cewa, daren Lailatul Qadr wata babbar dama ce ta tuba zuwa ga Allah daga zunubbanmu, wadda bai kamata mu yi saku-saku da ita ba.

Ya ci gaba da cewa, baya da falala da take a cikin watan ramadan, akwai falala ta musamman a cikin dararen Lailatul Qadr wadda ta ninka sauran falaloli da sauran ranaku da dararen da suke cikin wannan wata mai alfarama.

Malamin ya kara da cewa, ba ya ga ayyuka na nafila da mustahabbi, hatta ayyuka na wajibi Allah madaukakin sarki yana ninka ladarsu sau saba'in idan aka yi yi a cikin daren lailatul Qadr, da hakan ya hada da salloli na wajibi da zakka da sauransu.

 

 

3965731

 

captcha