IQNA

23:56 - May 04, 2021
Lambar Labari: 3485877
Tehran (IQNA) wata coci ta mabiya addinin kirista tana shirya wa musulmi buda baki a birnin Barcelona na kasar Spain.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa,  wata majami'ar mabiya addinin kirista tana shirya wa musulmi buda baki a birnin Barcelona na kasar Spain.

Tun daga lokacin da aka fara azumin watan ramadan, wannan majami'a tana gayyatar musulmi 50 zuwa 60 domin su zo su yi buda baki.

Cocin dai tana shirya abinci wanda yake halal a wajen musulmi domin musulmin su samu natsuwa dangane da abincin da suke wanda ya yi da addininsu.

Babbar manufar dai ita ce kara kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinan biyu domin kara samun zaman lafiya da girmama juna a tsakaninsu.

Hafez Ibrahim wani matashi ne musulmi dan shekaru 27 dan asalin kasar Morocco da yake zaunea  kasar Spain wanda daya ne daga cikin wadanda aka gayyata, ya bayyana cewa ya yi farin cikin ganin hakan, domin kuwa dukkanin addinan guda biyu suna yin kira zuwa ga zaman lafiya ne da kuma girmama fahimtar juna.

3969141

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: