IQNA

Shugaba Rauhani: Nan Ba Da Jimawa Za A Kawo Karshen Takunkuman Zalunci A Kan Iran

21:28 - May 05, 2021
Lambar Labari: 3485878
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba takunkuman zalunci da aka kakaba kan Iran za su kawo karshe.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, a jawabin da shugaba Hassan Rauhani ya yi a yau a taron majalisar ministocin kasar Iran a  birnin Tehran, ya bayyana cewa, al’ummar Iran za su ci gajiyar hakuri da kuma tsayin dakan da suka yi wajen kin mika wuya ga manufofin masu girman kai na duniya.

Ya ce nan ba da jimawa ba takunkuman zalunci da aka kakaba kan Iran za su kawo karshe, wanda hakan ke nufin cewa salon siyasar Amurka na kakaba ma Iran takunkumin domin karya ta ko kuma tilasta ta domin ta mika wuya, hakan bai yi nasara ba.

Shugaba Rauhani ya ci gaba da cewa, akwai ci gaba a tattaunawar raya yarjejeniyar nukiliya da ke gudana a birnin Viennan nakasar Austria, inda babban abin da yake da muhimamnci shi ne dukkanin bangarori su koma yin aiki da yarjejeniyar kamar yadda suka rattaba hannu a kanta.

Dangane da ranar Quds ta duniya kuwa, wadda za a gudanar a ranar Juma’a mai zuwa, Rauhani ya bayyana cewa, wannan rana tana a matsayin ranar makoki ga yahudawan sahyuniya, domin kuwa rana ce da ke tunatar da al’ummomin duniya baki daya halin kunci da suka jefa al’ummar Falastinu a ciki.

3969354

 

 

 

captcha