IQNA

23:35 - May 09, 2021
Lambar Labari: 3485896
Tehran (IQNA) 'yan ta'adda masu da'awar jihadi sun kashe fararen hula dukkaninsu mata a kasar Afghanistan da sunan jihadi.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon fashewar wani bam a wajen wata makaranta a Kabul babban birnin kasar Afghanistan.

Fashewar ta faru ne a unguwar da mabiya mazhabar Shi'a suka fi yawa a Dasht-e-Barchi, dake yammacin Kabul, ranar Asabar.

Kusan illahirin wadanda lamarin ya rusa dasu dalibai ne 'yan mata, inda kimanin hamsin daga cikinsu suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata.

Adadin zai iya fin hakan,”in ji kakakin ma’aikatar cikin gidan Afghanistan Tareq Arian, yayin da Gwamnatin Afgansitan ta yi tir da kakkausar murya da harin, ita kuma kungiyar Taliban ta musanta hannunta a harin.

sai dai bayan faruwar hakan kungiyar 'yan ta'addan nan ta Daesh mai dauke da akidar salafiyyar jihadiyya, ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai harin.

 

3970294

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Afghanistan ، mutum hamsin ، nnunta a harin. ، kungiyar taliban ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: