IQNA

Ofishin Ayatollah Sistani Ya Yi Kira Ga Al'ummomin Duniya Da Mara Baya Ga Al'ummar Afghanistan

23:40 - May 11, 2021
Lambar Labari: 3485904
Tehran (IQNA) ofishin Ayatollah sistani ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake kira da a taimaka ma al'ummar Afghanistan wajen tunkarar matsalar tsaro a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, ofishin Ayatollah sistani ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake kira da a taimaka ma al'ummar Afghanistan wajen tunkarar matsalar tsaro a kasar, wanda kan yi sanadiyar rasa rayukan fararen hula.

A cikin bayanin, ofishin ya yi tir da Allawadai da harin ta'addancin da 'yan ta'adda suka kai kan makarantar 'yan mata a birnin Kabul, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai kimanin 80 dukkaninsu 'yan mata wadanda shekarunsu ba su wuce ashirin ba.

Bayanin ya jara da cewa, aikin kungiyoyi irin wadannan na ta'addanci, ba ya wakiltar addinin musulunci ko musulmi ta kowace fuska, wannan aiki yana wakiltar wadanda suka aikata shi ne kawai.

Daga karshe ya kara jaddada kira ga dukkanin kasashen musulmi da su bayar da dukkanin gudunmawar da za su iya domin taimaka ma al'ummar kasar Afghanistan, domin tunkarar matsalar tsaro.

 

 

3970750

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ofishin Ayatollah Sistani ، taimaka ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :